Venezuela: 'Yan adawa sun zargi shugaba Maduro da mulkin kama karya

Masu zanga-zanga a Venezuela

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan adawa na ganin Mista Maduro ya yi wa kundin tsarin mulki karan tsaye

Tashin hankali ya sake barkewa a kasar Venezuela, a daidai lokacin da dubban masu zanga-zanga ke gudanar da gangami a daukacin kasar dan nuna adawa da gwamnatin shugaba Nicolas Maduro.

An samu rahoton harbe wani jami'in 'yan sanda, yayin da yawancin masu boren suka ji rauni saboda hayaki mai sa hawaye da jami'an tsaro suka yi amfani da shi dan tarwatsa masu zanga-zangar.

Wannan na zuwa ne kwana guda da 'yan adawa kuma masu rinjaye a majalisar dokokin kasar suka kada kuri'ar amincewa da tuhumar shugaba Maduro da suke zargi da yi wa dimukradiyya hawan kawara.

Shi kuma ya zargi 'yan majalisar da yunkurin yi masa juyin mulki.

A bangare guda kuma gamayyar jam'iyyun adawa a Venezuela, sun yi kiran magoya bayansu su shiga yajin aiki na sa'o'i goma sha biyu ranar Juma'a.