'Mutum na gab da karar da halittun duniya'

Nau'in giwayen Afurka

Asalin hoton, WWF

Bayanan hoto,

Yawan giwayen Afurka ya ragu matuka saboda farauta

Wani rahoto mai tayar da hankali na hadin guiwa da kungiyar kare halittu da muhalli ta WWF, da ta kare dabbobi ta Zoological Society ta Landan ya nuna cewa dan-adam ya karar da kashi 60 cikin dari na dabbobi masu kashin baya a duniya tun daga 1970.

Rahoton ya yi gargadin cewa idan lamarin ya ci gaba da kasancewa haka za a wayi gari an kawar da tsarin cude-ni-in-cude ka da halittun duniya gaba daya suka dogara a kansa ya gushe.

Masu binciken da suka hada rahoton sun yi nazarin bayanai kan kusan nau'in dabbobi ko halittu daban-daban har 4000.

Rahoton ya gano cewa sha'awa ko marmarin dan-adam, halittar da yawanta ya linka biyu a shekara 50 da ta wuce, yana cinyewa da cunkushewa da kuma gurbata abokan zamansa na duniya har su kare.