Fari ya jefa mutum miliyan 1.5 cikin yunwa a Madagascar

Karancin abinci a Madagascar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Farin shekara uku a jere ya jawo karancin abinci a Madagascar

Majalisar dinkin duniya ta ce mutane kusan miliyan daya da rabi a kudancin Madagascar na fuskantar yunwa, sakamakon matsanancin fari.

Hukumar abinci ta majalisar dinkin duniya ta ce an samu raguwar kayan amfanin gona dangin cimaka matuka, a kudancin katafaren tsibirin.

A wani yanki guda daya, yawan masarar da ake nomawa ya ragu da kashi 80 cikin dari a wannan shekarar, shi kuwa yawan rogon da ake girba a yankin ya kasance kusan rabi kawai aka samu a bana.

Shinkafa ma ta ragu zuwa kashi 60 cikin dari kan yadda aka saba girba, a wasu yankunan, inda hakan ya sa jama'a suka karkata wajen siyo ta daga waje.

Wannan matsala ta karancin cimaka ta kuma jawo tashin farashin kayan abinci a tsibirin, yayin da wasu mutanen suka koma cin 'ya'yan itatuwan daji, suna kuma sayar da dabbobinsu da kayan aikinsu na gona domin su rayu, wanda hakan ke nufin girbin badi shi ma zai kasance cikin rashin tabbas.

Majalisar dinkin duniya ta ce sama da rabin mutanen da ke a wannan hali, suna cikin tsananin matsalar karancin abinci, abin da ke nufin suna abukatar taimako.

Hukumar abinci da aikin gona ta majalisar dinkin duniya, wadda ke aiki tare da shirin samar da abinci na majalisar, ta ce, za ta taimaka wa jama'a da kananan gonaki a yankunan da farin ya fi kamari.

Ta ce za ta taimaka da abinci da irin shuka da kayan aikin gona, domin manoman su ribaci damunar da ke tafe, wadda za ta fara a yankin a watan Nuwamba.

Wasu kasashen Afurkan ma sun shiga irin wannan matsala ta tsananin fari a baya bayan nan, wadda annobar sauyin yanayi ta El nino ta kara kamarin matsalar.