Malawi: Majalisar Coci-Coci ta amince da zubar da ciki

Peter Mutharika

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wasu kungiyoyin addinai har yanzu na adawa da dokar ta gwamnatin Shugaba Mutharika

Majalisar coci-coci ta Malawi, ta mara baya ga gyare-gyaren da aka yi wa dokokin zubar da ciki na kasar masu tsauri, wadanda za su ba da damar zubar da cikin bisa wasu dalilai.

Dalilan sun hada da cikin da aka samu ta hanyar fyade, ko idan dan-tayi ya samu nakasa, ko kuma idan lafiyar matar na cikin hadari.

A yanzu dai laifin zubar da ciki ya tanadi hukuncin zaman gidan yari da ya kai har shekara goma sha hudu.

Kungiyar ta coci-coci wadda ta kunshi mabiya darikar Katolika da na Furotesta (Protestant), ta ce ta goyi da bayan sauyin ne, saboda mata da yawa suna mutuwa yayin zubar da ciki ta hanyoyin da ba su dace ba.

Wasu kungiyoyin addini na kasar ta Malawin har yanzu suna adawa da sauye-sauyen dokar.