Buhari ya yi martani kan kin karbar mukamansa

Shugaba Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gwamnatin Buhari ta ce, ba wanda ba a tuntuba ba domin ba shi mukami

Fadar shugaban Najeriya ta ce shugaban kasar ba ya tura wa majalisar dattawa sunayen mutanen da yake so a nada musu mukami a gwamnatinsa, sai ya bi dukkan hanyoyin tuntuba.

Fadar dai tana mayar da martani ne dangane da matakin da wasu daga cikin mutanen da aka mika wa majalisa sunayensu suka dauka na kin karbar tayin aiki da gwamnatin Buharin kan, lamarin da ya sa masana zargin cewa gwamanti na ayyana sunayen ne ba tare da tuntuba ba.

Mallam Garba Shehu, mai taimaka wa shugaban kasar a kan harkokin yada labarai, ya shaida wa BBC cewa masu cewa ba a tuntube su ba, suna kokari ne su shafa wa gwamnati kashin-kaji kawai.

Ya ce game da Uwargida Paulin Tallen daga jihar Filato, jinkiri aka samu na dan sakon da gwamnati ta tura mata har aka yi sanarwar, shi kuwa Dakta Usman Bugaje, kakakin ya ce ya gaya musu a shirye yake ya yi aiki da gwamnatin, amma kuma ya riga ya karbi wasu ayyuka a kasashen waje, da ba zai yiwu ya hada biyun ba.