Ba za mu kori Rooney ba —Mourinho

Rooney ba ya jin dadin rashin sanya shi a wasa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Rooney ba ya jin dadin rashin sanya shi a wasa

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce babu inda kyaftin din kungiyar Wayne Rooney zai je.

Mourinho ya yi watsi da rahotannin da ke cewa an gaya wa dan wasan ya fice daga Old Trafford zuwa wata kungiyar idan yana so a rika sanya shi a wasa.

Rooney, mai shekara 31, bai buga wasannin lig ba tun bayan fafatawar da ta yi da Watford inda suka tashi da ci 3-1 ranar 18 ga watan Satumba, kuma bai shiga wasannin biyu na karshe da kungiyar ta yi ba saboda ya ji rauni.

Mourinho ya shaida wa 'yan jarida cewa,"Babu wata matsala da dan wasan ke fuskanta, amma na san kun rubuta labaranku ne domin ku sayar da jaridunku."

A cewarsa,"Rooney babban dan wasa ne wanda ke da matukar muhimmanci a gare mu. Babu inda za shi- muna kaunarsa. Ba ya jin dadi ne kawai saboda an bar shi a benchi sannan kuma ya ji rauni."

Yanzu dai Rooney ya murmure daga raunin da ya ji.

Kwallaye hudu ne kawai suka rage masa, wadanda idan ya zura su zai wuce Sir Bobby Charlton wanda ya zura wa United kwallaye 249, ya zama gagara-badau.

But he has scored just once this season and has not found the net in his last 10 games for United.

Mourinho ya kara da cewa 'yan jarida sun yi masa kazafi da suka ce zaman da yake yi shi kadai a Manchester tamkar wani "bala'i" ne ya same shi.