'Yan tawayen Syria sun kai babban hari a Aleppo

Asalin hoton, Reuters
Rahotanni sun ce kungiyoyin 'yan tawaye da ke Aleppo, ciki har da tsohuwar kungiyar al-Nusra sun goyi bayan farmakin
'Yan tawayen Syria sun sanar cewar sun kai wani gagarumin hari da nufin kawar da kawanyar da dakarun gwamnatin kasar suka yi a yankunan gabashin Aleppo da ke karkashin ikonsu.
Wata kungiyar da ke sanya ido kan rikicin Syria wacce ke Burtaniya ta ce 'yan tawayen sun harba daruruwan makamai masu linzami a yammacin Aleppo,lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutum 15.
Rahotanni sun ce sun kai hari kan filin jiragen saman sojoji na al-Nayrab zuwa gabas.
Dakarun da ke goyon bayan gwamnati sun kwashe wantanni suna kawanya da kusan mutum 275,000 a gabas.
Syria da kawarta Rasha sun tsananta hare-haren sama a gabas a baya bayan nan.
A halin yanzu dai, hare-haren na zuwa ne daga wurin 'yan tawayen da ke wajen Aleppo amma kuma an gano cewa 'yan tawayen da ke cikin birnin za su mara musu baya.