Ana rikici kan limancin Masallacin Sultan Bello

Sarkin Zazzau shi ne shugaban addinin musulmi a jihar
Bayanan hoto,

Babu rahoton raunata kowa a rigimar

Rundunar 'yansanda a jihar kaduna ta Najeriya ta ce ta kama mutane 14 a yayin wata hatsaniya da aka yi kan limacin masallaci mafi girma a jihar- wato masallacin Sultan Bello.

Rikicin ya barke ne yayin sallar Jumu'a tsakanin magoya bayan Sheikh Ahmad Mahmud Gumi da na Dokta Khalid Aliyu wanda aka nada a matsayin limamin masallacin na bayan tube limamin na baya.

Magoya bayan Sheikh Ahmad Gumi na adawa da nadin Dokta Khalid ne a zaman limamin masallacin inda suke ganin gwanin nasu ne ya kamata a nada.

Duka manyan malaman biyu dai sun dora alhakin tashin hankalin kan junansu.

A wani taron manema labarai daya daga cikin kungiyoyin musulmi mafi girma a kasar - Jama'atul Nasril Islam ta yi Allah-wadai da wannan lamari,inda ta yi kira ga gwamnati ta sa baki kafin alamurra su kazance.