Zan daure masu kokarin tsigeni, in ji Maduro

Shugaba Nicolas Maduro ya ce yajin aikin da 'yan adawa suka kira bai yi nasara ba
Bayanan hoto,

Shugaba Nicolas Maduro ya ce yajin aikin da 'yan adawa suka kira bai yi nasara ba

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya yi barazanar daure abokan hamayyarsa a gidan yari idan har suka zauna domin kada kuri'a da nufin cire shi daga kan mukaminsa.

Shugabannin 'yan adawar sun yi alkawarin cewa za su kada kuri'a a kan sa bayan da yunkurinsu na gudanar da kuri'ar raba gardama akan tsige shugaba Maduro ta samu cikas.

Mr. Maduro ya ce yajin aikin da suka kira bai yi nasara ba, kuma mafi yawancin manyan wuraren aiki a kasar sunyi aiki kamar yadda suka saba.

'Yan adawar dai na zargin shugaban kasar da yi wa tattalin arzikin kasar rikon-sakainar-kashi.