Zan kulle masu yunkurin tunbukeni daga kan mulki- Nicolas Maduro

Mr Maduro ya ce yajin aikin aikin da aka kira bai yi tasiri ba
Bayanan hoto,

Mr Maduro ya ce yajin aikin aikin da aka kira bai yi tasiri ba

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya yi barazanar kulle abokan hamayyarsa a gidan yari idan har suka zauna domin kada kuri'a da nufin cire shi daga kan mukaminsa.

Shugabannin 'yan adawar sunyi alkawarin cewa za su kada kuri'a akansa bayan da yunkurinsu na gudanar da kuri'ar raba gardama akan tsige shugaba Maduro ta samu cikas.

Mr maduro ya ce yajin aikin da suka kira bai samu nasara ba, kuma mafi yawancin manyan wuraren aiki a kasar sunyi aiki kamar yadda suka saba.

Yan adawar dai na zargin shugaban kasar da yiwa tattalin arzikin kasar rikon sakainar kashi.