Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya 5, sun raunata 19

Motar Sulke ta sojan Najeriya
Bayanan hoto,

Tuni dai aka kwashe wadanda harin ya rutsa da su zuwa birnin Maiduguri.

Rundunar sojan kasa ta Najeriya ta ce sojojinta biyar sun mutu wasu kuma 19 suka samu raunukka a cikin wani kwanton-bauna da mayakan Boko Haram suka yi musu a kudancin jihar Borno.

Wata sanarwa daga kakakin rundunar Kanal Sani Usman Kukasheka ta ce lamarin ya faru ne a kauyen Ugundiri da ke cikin yankin karamar hukumar Damboa lokacin da suke dawowa daga wajen wani aikin kakkabe mayakan kungiyar a kudancin jihar.

Sanarwar ta ce haka ma wasu 'yan banga uku da mayakin sa-kai daya sun rasa rayukkansu a cikin harin na ranar Assabar.

''To amma duk da haka su 'yan Boko Haram din an kashe 18 daga cikinsu kuma an lalata wata mota mai dauke da bindiga mai sarrafa kanta.'' In Ji Kanal Kukasheka a cikin wata hira da BBC.

Harin dai ya zo ne a daidai lokacin da wasu 'yan kunar bakin wake da ake tunanin 'yan kungiyar ne suka kai hare-hare a kusa da birnin Maiduguri abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tara.