Fursunoni 143 sun tsere a Chadi

Fursunoni 143 ne suka tsere daga gidan yarin Abeche
Bayanan hoto,

Fursunoni 143 ne suka tsere daga gidan yarin Abeche

Jami'an tsaro a abirnin Abeche na kasar Chadin na cigiyar ragowar fursunoni su 118 daga cikin 143 da suka tsere daga gidan yari a makon jiya.

Rahotanni na cewa fursunonin sun tserene bisa zargen cewa suna fuskantar karancin abinci, a yayin da kuma a wani bangare ake cewa zabin abincin da suke yi ne ya sa suka tsere.

Abinda ya haddasa ya mutsin da ya sa fursunonin tserewa shi ne rashin ingancin abincin da ake ba su, yayinda wasu kuwa ke cewa abincin ne ma kwata-kwata ba bu.

A bangare guda kuwa, ana zargin cunkoson da ake dashi a gidan yarin ma ya haddasa tserewar fursunonin.

Sai dai hukumomi sun samu kamo 25 daga cikin fursunonin.