India: Bukukuwan Diwali sun bar baya da kura

Asalin hoton, AP
Mahukunta a Delhi sun yi gargadi kan gurbatar iska gabanin bukukuwan na Diwali
Mazauna birnin Delhi na kasar India da suka fusata, na ta musayar hotunan hazon da ya turnuke birnin, kwana guda bayan bukukuwan Diwali inda aka yi gagarumin wasan wuta.
Hazon wanda kurar launikan da aka rika watsawa sama ta haifar, ya gurbata iskar da ke da mummnar illa ga jama'a.
Mahukunta sun yi gargadin cewa birnin Delhi za su fuskanci gurbatacciyar iska saboda yanayin zafi da kuma iska mai sauri da ke kadawa.
Dawali wani muhimmin lokacin bukukuwa ne na Hindu a arewacin India, inda ake murnar nasarar da aka samu kan aikata laifuka.
Ana kuma wasan wuta ne a lokacin irin wadannan bukukuwa, amma kuma hakan na gurbata iska mai kyau.
A makon jiya ne hukumomi a birnin na Delhi suka sanar da cewa za su kakkafa wasu na'urorin tace gurbatacciyar iska a bakin hanyoyi don rage gurbatarta.