Shugaban jam'iyyar Democrat ya ce 'FBI da karya doka'

Hillary Clinton da James Comey

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Mr Comey na fuskantar matsin lamba daga jam'iyar Democrat kan matakin da ya dauka

Shugaban jam'iiyar Democrat a majalisar dattawan Amurka ya ce hukumar bincike ta FBI ta karya doka, kan binciken da take yi game da sakonnin E-mail da ke da alaka da 'yar takarar shugabancin kasar Hillary Clinton.

Harry Reid ya zargi daraktan hukumar ta FBI James Comey da sabawa dokar da ta hana jami'anta yin katsalandan a harkar zabe.

Rahotanni game da binciken hukumar ta FBI na zuwa ne makonni biyu kafin zaben da za a gudanar a Amurka.

Hukumar ta samu takardar izinin binciken tarin sakonnin E-mail din mataimakiyar Mrs Clinton Huma Abedin, da aka gano a cikin na'urar komfiyutar maigidanta.

Sakonnin E-mail kimanin 650,000 ne za a gudanar da bincike a kan su, da ake ganin zai yi wuya masu binciken su fitar da sakamako a kan su kafin ranar zabe.

Hukumar ta FBI ta ce tana da yakinin cewa sakonnin E-mail din za su iya kasancewa suna da alaka da binciken da gudanar a baya kan Misis Clinton.

Ita dai Clinton ta yi amfani da yanar gizo ta musamman a lokacin da take rike da mukamin sakatariyar harkokin wajen Amurka a gwamnatin Shugaba Barack Obama.