Dakarun Iraki sun shiga birnin Mosul

Dakarun Iraki na fuskantar turjiya daga mayakan IS a birnin Mosul
Dakarun Iraki na musamman sun kutsa cikin birnin Mosul, inda suke yin bata-kashi da mayakan kungiyar IS da ke rike da ikon birnin.
Mayakan IS din na ta harba rokoki, da gurneti da karin wasu kananan makamai, tare da amfani da mota wajen kaddamar da hare-haren kunar bakin wake.
Wakilin BBC Ian Pannell wanda ke tare da sojojin gwamnati, ya ce suna fuskantar kazamar turjiya daga mayakan IS.
Jiragen yakin dakarun kawancen da Amurka ke jagoranta sun kaddamar da hare-hare hudu ko biyar ta sama don taimakawa dannawar da dakarun Irakin ke yi cikin birnin.
Tun da farko Fira Ministan Iraqi Haider al-Abadi, sanye da kakin soji, ya yi kira ga mayakan na IS da su mika wuya ko kuma su bakunci lahira.
Yayin da yake magana a wani sansanin sojin sama a arewacin Iraqi, Mr al-Abadi, ya ce dakarun da gwamnati ke jagoranta na kara dannawa ta ko wacce kusurwa, yana cewa za su "datse kan maciji".
Wannan dai wani bangare ne na fafutukar kwato birnin, wacce aka kaddamar makonni biyu da suka wuce.