Nigeria: Sanatoci sun yi watsi da shirin Buhari na ciyo bashi

Majalisar dokokin Najeriya
Bayanan hoto,

Babu tabbas ko Shugaba Buhari zai sake aika bukatar

Majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da bukatar Shugaba Muhammadu Buhari ta karbo bashin dala biliyan 30 domin gudanar da wasu manyan ayyuka a shekaru biyu masu zuwa.

A makon da ya gabata ne shugaban ya nemi amincewar majalisar domin ranto wadannan kudade daga kasashen waje, inda aka gabatar da ita a zaman majalisar na ranar Talata.

Wata majiya ta shaida wa BBC cewa sanatocin sun yi watsi da bukatar shugaban ne saboda rashin yi musu cikakken bayani kan hanyoyin da za a bi wurin biyan bashin.

Shugabana majalisar dattawan Bukola Saraki ya yi mamakin matsayin sanatocin, abin da ya sa ya nemi amincewar su har sau biyu, amsa suna cewa ''a'a''.

A don haka Sanata Saraki ya yanke hukuncin da ya yi daidai da muradun mafi rinjayen sanatocin da suka nuna rashin amincewa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Matsalar tattalin arzikin da Nigeria ta shiga na daga cikin dalilan karbo bashin

Wannan ba karamin koma baya ba ne ga Shugaba Buhari, wanda ke fatan samun kudaden zai taimaka a yunkurinsa na fitar da kasar daga cikin matsin tattalin arziki.

Rancen na kasashen waje dai ya kunshi dala biliyan 11 da miliyan 200 na gudanar da wasu ayyuka, da rancen gudanar da ayyukan samar da ababen more rayuwa na musamman wanda ya kai dala biliyan 10 da 600.

Akwai kuma takardun lamuni na Turai wadanda darajarsu ta kai dala biliyan hudu da rabi, da kuma tallafi ga kasafin kudi na gwamnatin tarayya wanda ya kai dala biliyan uku da rabi.

Cinikin danyen man fetur ne ke samar da kashi biyu bisa uku na kudin da gwamnatin Najeriyar ke samu, lamarin da ya sa kasar ta fada matsalar tattalin arziki sakamakon faduwar farashin danyen man fetur a kasuwannin duniya.