Za a hukunta duk wanda karensa ya yi kashi a hanya

Karnuka a Spaniya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Gwajin kwayoyin halittar karnuka a Spaniya don tsaftace gari

Mahukunta a gundumar Valencia da ke kasar Spaniya za su kaddamar da matattarar bayanan kwayoyin halitta na karnuka, don kama wanda ya bar karensa ya yi kashi a kan hanya.

Jami'ai a birnin Mislata sun bayyana cewa masu sharar titi za su rika bi suna daukar samfurin kashin karnukan zuwa dakunan bincike don tantancewa.

Don haka ya zama dole masu karnukan su kai su wurin likitocin dabbobi don yi musu rijistar kwayoyin halitta.

Sun kuma ce duk wanda bai yi hakan ba za a hukunta shi.

Daga watan Janairu duk masu karnukan da suka ki share kashin karnukan na su za a rika bin diddiginsu a kuma ci su tararsu.