China ta kaddamar da jiragen yaki masu layar zana

Jirgin yaki China
Bayanan hoto,

China ta ce za ta kara bajakolin wasu kayayyakin fasahar nan gaba

Kasar China ta kaddamar da wasu jiragen yaki biyu da ta kirkiro wadanda suka fi ko wanne fasaha a wani taro a kudancin birnin Zhuhai.

Wadannan Jirage sun dau hankulan manyan baki, da 'yan kallo, da kuma jagororin masana'antu a bikin kaddamarwar.

Jiragen da aka yiwa lababi da J-20 na da wata fasahar da za ta hana iya gano su a duk inda suke.

Don sirri da kuma kare satar fasaha, ba a bai wa mutane izinin kallon jiragen a kasa ba.

Za kuma a yi baje kolin wasu kayan aikin sojin a wani taro mafi girma na kasar ta China.

Wadannan kaya za su hada da na'urorin binciken jirage da kasar ke fatan sayarwa baki 'yan kasashen waje.