Sojojin Nigeria sun murkushe harin bam a Gubio

Boko Haram Nigeria

Asalin hoton, Nigeria Army

Bayanan hoto,

A motar a-kori-kura aka yi niyyar kai harin

Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun murkushe wani yunkurin kai hare-haren kunar bakin wake a garin Gubio da ke arewacin jihar Borno.

Wta sanarwar da runudunar ta fitar ta ce "dakarun soji sun dakile 'yan kungiyar Boko Haram takwas da ke cikin wata motar a-kori-kura makare da ababan fashewa".

Maharan sun yi kokarin kutsa wa ta cikin shingayen ababan hawa, amma ojin suka jajirce a kan sai sun yi binciken kwakwaf.

Hakan ya sa suka tarwatsa kansu ta hanyar tayar da daya daga cikin rigunan bam din da ke cikin motar, inda dukkansu suka hallaka.

Wannan ne harin kunar bakin wake na hudu a cikin kwanaki uku a birnin Maiduguri, cibiyar kungiyar ta Boko Haram.

Sama da mutane 20,000 ne suka mutu sakamakon rikicin na Boko Haram, wanda aka shafe shekara bakwai ana yi.

Kimanin wasu sama da miliyan biyu kuma sun bar gidajensu, inda wasunsu ke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira.