Habasha ta fara mika wuya ga masu yi mata bore

Oromo Habasha

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

'Yan kabilar Oromo na kasar Habasha sun sha yiwa gwamnati bore kan mayar da su saniyar ware

Habasha ta fara mika wuya ga 'yan kabilar Oromo masu yi mata bore kan mayar da su saniyar ware a fannoni da dama.

Yanzu dai ta fara bai wa wasu daga cikin su mukamai a gwamnatinta.

Praministan Habasha, Hailemariam Desalegn, ya bayyana sabuwar majalisar zartarwar kasar ya yin da ake ta zanga zangar siyasa wadda ta kai ga sa dokar ta baci a kasar.

An maye guraban da yawan sanannun ministocin da kwararru.

Mr Desalegn ya ce babban abin da aka yi la'akari da shi a zaben ministocin shi ne na cancanta da kwatanta gaskiyarsu da ma hanzarin yiwa jama'a aiki.

Wannan ita ce majalisar zartarwa ta farko da ta kunshi mutanen da ba 'yan kabilar Tigrayan da suka mamaye gwamnatin hadakar.

Sabon ministan harkokin waje dan kabilar Oromo ne, wadanda ke sahun gaba a rikicin da akai ta tyi na baya bayanan.

Sabon mai magana da yawun gwamnati wanda shi ma dan Oromo ne, ya ce sauyin ya zama tilas bayan fadace fadancen da aka yi ta yi.