'Yan Niger Delta sun mika bukatunsu ga gwamnati

Hare-haren Avengers dai sun taimaka wajen kassara tattalin arzikin Nigeria
Bayanan hoto,

Hare-haren Avengers dai sun taimaka wajen kassara tattalin arzikin Nigeria

Dattawan yankin Niger Delta a Nigeria sun gabatar wa Shugaba Muhammadu Buhari shawarwari 16 da suka ce za su taimaka wurin samar da zaman lafiya a yankin.

A ranar Talata ne shugaban ya gana da wakilan masu tayar da kayar baya da kuma shugabannin al'umma da nufin kawo karshen hare-haren kan bututan mai a yankin.

Shugaban ya shaida wa tawagar cewa matsalolin da gwamnatinsa ta tarar a lokacin da ta karbi mulki suna da yawan gaske, wadanda suka hada da faduwar farashin mai, da kasa biyan albashi a jihohi 27 daga cikin 36 na kasar.

Sauran matsalolin a cewar shugaban Najeriyar sun hada da rashin tattalin dan abun da kasar ke samu, lamarin da ya ce babu yadda za a yi a ci gaba da tafiya a haka.

Hare-haren kungiyoyi irin su Niger Dealta Avengers sun taimaka wajen kassara tattalin arzikin kasar.

Jerin bukatun da tawagar ta gabatar sun hada da gaggauta kammala manyan hanyoyin da aka fara a yankin da kuma mayar da hedkwatar manyan kamfanonin mai a Nigeriar zuwa yankin Niger Delta, matakin da a cewarsu zai taimaka wajen kara samar da ci gaba a yankin.

Shugabannin yankin Niger Deltan karkashin jagorancin Chief Edwin Clerk sun kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta share dagwalon mai da ya mamaye wasu garuruwa a yankin baya ga yankin Ogoni.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Haka kuma Shugabannin sun nemi gwamnati da ta sake duba shirin afuwa ga tsagerun yankin tare da tabbatar da cewa an samar da ayyukan yi ga wadanda aka horas da su karkashin shirin yin afuwa ko kuma a rika ba su dan abun hasafi.

Sun kuma sha alwashin ci gaba da tattaunawa akai-akai a jihohi daban-daban na yankin a wani mataki na ganin an samu dorewar zaman lafiya.

Sannan suka ce tuni aka fara ganin tasirin tattaunawar da suke yi tsakaninsu wanda hakan ya kai ga yanzu aka samu karuwar danyen mai da ake hakowa zuwa sama da ganga miliyan biyu.

Shugaba Buhari wanda ya ce yana jiran rahoton wani kwamitin da ya dora wa alhakin sake nazari a kan shirin yin afuwa ga tsegurun yankin Neja Delta, inda daga nan ne gwamnatin sa za ta ga bangaren da ta gaza domin yin gyara.

Tawagar karkashin kungiyar Pan Niger Delta Forum ta kuma jaddada goyon bayanta ga Shugaba Buhari bisa abin da ta ce kokarin gwamnatinsa wajen tabbatar da hadin kan al'ummar Nigeria a matsayin kasa daya.