Bukatar Musulumi ta cire sunan alade a manhaja ta jawo ce-ce-ku-ce

Hedikwatar kamfanin Alibaba, a China

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Alibaba na daya daga cikin kamfanonin sayar da kaya ta intanet da suka shahara a duniya

Kiran da wani Musulmi ya yi ga katafaren kamfanin sayar da kaya ta intanet na China, Alibaba, kan ya sauya sunan wata manhajarsa ta sayen tikitin tafiye-tafiye ta intanet, saboda sunan ya kunshi kalmar alade, ya jawo ce-ce-ku-ce.

Tun da farko dai kamfanin ne ya sauya sunan mashigar manhajarsa (app) ta sayen tikitin tafiye-tafiye, mai farin jini, daga Alitrip zuwa wani sunan da ke nufin alade me tashi a harshen Sinanci (''Flying Pig'').

Daga nan ne kuma wani Musulmi dan kasuwa dan kasar ta China, Adil Memettur, ya soki matakin sanya sunan aladen, a wani shafinsa na intanet mai suna Sina Weibo, inda yake da dubun dubatar mabiya.

Ya nuna cewa manhajar tana da farin jini ne a tsakanin kabilu da sauran mutane marassa rinjaye, saboda a tsarinta ana ba mutanen da rubutun sunansu yake daban da na yawan mutane su sayi tikiti ta intanet.

A rubutun da ya yi a shafin nasa, dan kasuwar ya ce, '' ina ganin tun da yanzu Alitrip ya sauya sunansa zuwa alade mai tashi, zan cire shi daga wayata, kuma ina ganin ya kamata dukkanin abokanaina su ma su cire, saboda kalmar alade haramun ce ga Musulmin duk duniya. Alibaba kamfani ne na duniya ko zai yi la'akari da abin da ya saba wa Musulmi?''

Bayyanar wannan rubutun nasa ke da wuya sai aka fara sukansa da yi masa habaici a suaran shafukan kasuwanci ta intanet, inda wasu kamfanonin ke cewa, to hakan na nufin kenan China, ta cire duk inda aka sanya wani suna ko alama ko wani abu da ya shafi alade a al'adunta.

Alibaba ya shaida wa BBC cewa ya yanke shawarar sauya sunan mashigar manhajar sayen tikitin tafiye-tafiyen ne ta intanet, domin ya samu karbuwa ga matasa.