Koriya ta Kudu: Park na binciken aminiyarta

Asalin hoton, Getty Images
Danbarwar kudaden ta hada da aminiyarta tun ta kuruciya
Shugabar kasar Koriya ta Kudu Park Geun-Hye, ta sauya Firaiminista da Ministan kudin gwamnatin ta, a kokarin kaucewa danbarwar siyasa da ta hada da wata aminiyarta.
Ana zargin kawar ta mai suna Choi Soon-sil, da kokarin amfani da ita dan cimma manufar samun kudade, kuma tuni aka tsare ta saboda gudun kar ta yi kokarin tserewa daga kasar.
Wakilin BBC yace shugaba Parka na cikin tsaka mai wuya saboda masu shigar da kara sun gurfanar da kawar ta da suka shafe shekaru 40 tare gaban kuliya, ana tuhumar ta da ko ta na amfani da kawancen da ke tsakanin ta da shugabar kasar ta hanyar samun kudade daga kamfanonin.
Wakilin ya kara da cewa ba a bayyana ko ministocin an sallame su daga bakin aiki ba, ko kuma su ne suka zabi barin aiki, ko kuma an same su da hannu a badakalar da ta taso ba.