Buhari zai sake mika neman rance ga Majalisar dattawa

Shugaba Buhari na son karbar rancen dala biliyon 30 daga waje don cike gibin kasafin kudi

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaba Buhari na son karbar rancen dala biliyon 30 daga waje don cike gibin kasafin kudi

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce zai mika wa `yan majalisar dokokin kasar cikakken bayanin da suke nema domin samun amincewarsu dangane da bukatarsa ta karbar rancen dala biliyon 30 daga waje don cike gibin kasafin kudin kasar na shekaru uku masu zuwa.

A ranar Talata ne majalisar dattawan kasar ta yi watsi da bukatar shugaban Buharin saboda ba a yi musu bayani a kan sharudan da ke tattare da bashin ba.

Mai taimaka wa shugaban kasar a kan harkokin majalisar wakilai, Hon Kawu Sumaila ya ce nan bada jima wa bane shugaban kasar zai sake gabatar da cikakken bayani ga Majalisar.

'Yan majalisar dattawan dai sun ce shugaban kasar bai yi musu cikakken bayani ba a kan sharudan da ke tattare da bashin.

Shirin rancen dai ya hada da sayar da takardun bashi na kudin Euro da kuma shirin tallafawa kasafin kudi.