Mutane 18 sun mutu a rikici tsakanin Fulani da Manoma a Niger

Fulani makiyya
Bayanan hoto,

Rikici akan gonaki tsakanin Fulani makiyya da manoma ya zama tamkar ruwan dare a kasashen yammacin Afirka

A Jamhuriyar Niger, a kalla mutane 18 ne suka mutu yayin da wasu 20 suka jikkata a wani kazamin fada daya barke tsakanin manoma da makiyaya a jahar Tawa.

Jami'ai sun ce rikicin ya barke ne kusa da wani kauye mai suna Bangui, da ke kudancin kasar.

Monoman dai na zargin Fulanin da barin dabbobinsu shiga wasu gonaki tare da lalata musu amfanin gona.

Rikici akan gonaki da sauransu tsakanin Fulani makiyya da manoma ya zama tamkar ruwan dare a kasashen yammacin Afirka, lamarin da kan kai ga asarar rayuka.