El-Rufai ya sasanta rikicin masallacin Sultan Bello

Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai
Bayanan hoto,

Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya ba wa kwamitin makonni biyu ya nada sabon limami

Bangarorin da ke rikicin shugabanci a kan masallacin Sultan Bello da ke Kaduna sun sasanta bayan da gwamnatin jihar ta shiga tsakani.

Matakin da gwamnan jihar ya dauka shi ne na cewa a bar mataimakin limamin ya ci gaba da limanci a matsayin wucin-gadi kafin a nada limami na din-din.

Kwamitin masallacin bisa hadin guiwa da Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, da kungiyar Jama'atu Nasril Islam da bangaren Dakta Ahmad Gumi da sauran masu ruwa da tsaki su aka dora wa alhakin nada sabon limamin.

A wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Samuel Aruwan, ya fitar, ya ce, an kawo karshen rikicin ne bayan wani zama da bangarorin suka yi a gidan gwamnati, wanda gwamnan jihar Nasir Ahmad El-Rufai ya shirya.

Sanarwara ta ce bayan da gwamnan ya ji bayanin dukkanin bangarorin da ke rikicin, ya ce gwamnati ta shiga tsakani ne saboda tsaro kawai, amma ba domin wani abu ba.

Sannan ya yi gargadin cewa gwamnati ba za ta lamunta da duk wani mataki na karya doka ba da sunan addini, da kuma barin mutane suna nema wa kansu mafita ba kan wata matsala.