Shugaba Jacob Zuma na fuskantar sabon zargin rashawa

Sama da shekara 10 shugaban na fama da zargin rashawa, abin da yake musantawa
Wani bincike da aka gudanar kan zargin cewa Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu yana huldar da ba ta dace ba da wasu hamshakan 'yan kasuwa, ya ce ya gano wata shedar almundahana kan shugaban.
Rahoton wanda aka dade ana jiran fitowarsa ya bukaci Shugaba Zuman ya kafa kwamitin bincike na shari'a cikin kwana 30, kan abubuwan da aka gano.
Asalin hoton, GALLO IMAGES
A da dan Jacob Zuma, Duduzane (a dama) abokin kasuwancin iyalan Gupta ne
Tun da farko Shugaban ya janye wata kara da ya shigar, wadda yake neman hana ko jinkirta fitar da rahoton, wanda wani bangarensa ya binciki alakarsa da hamshakan attajiran 'yan kasuwar nan da ake kira iyalan Gupta.
Rahoton mai shafi 355 ya bukaci da a kara bincike a kan zargin almundahana, da ya hada da sayen wani wurin hakar ma'adanai da kamfanin Teget, wanda dan Shugaban, Duduzane Zuma, ya mallaki wani bangarensa ya yi.
Asalin hoton, AP
Sun lashi takobin ci gaba da zanga-zanga har sai sun kawar da Shugaban
'Yan sanda sun yi amfani da gurneti-gurneti na roba domin tarwatsa masu zanga-zanga da ke neman Shugaban ya sauka daga mulki.
Sama da shekara goma Shugaban kuma jagoran jam'iyyar ANC, yake fama da zargin cin hanci da rashawa, abin da a kullum yake musantawa.