An sake yin girgizar kasa a Italiya

Girgizar kasar da ta faru a Italiya a watan Agusta ta yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane dari uku
Kasar Italiya ta sake fuskantar wata girgizar kasar, kwanaki uku bayan wata girgizar kasa da ba a taba ganin irinta ba cikin fiye da shekaru talatin da biyar ta afkawa kasar.
Wani bincike da kwararru na Amurka suka gudanar ya nuna cewa sabuwar girgizar kasar da ta afkawa tsakiyar kasar, bata kai karfin wadda ta faru ba a baya kuma kawo yanzu babu wani rahoton barnar da ta yi.
Lamarin dai ya faru ne a kusa da kauyen Pieva Taroni da ke kan tsaunin kudu maso gabashin birnin Perugia.
Yawancin mazauna yankin dai sun yi gaggawar barin kauyukan su tun bayan girgizar kasar da ta faru tun a watan Agusta da ya wuce, da aka yi asarar rayukan sama da mutane dari uku.