Nigeria: 'Ba son kai a yaki da cin hanci'

Shugaba Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya sha alwashin magance cin hanci da rashawa a kasar

Gwamnatin Nigeria ta musanta zarge-zargen cewa tana nuna son kai da siyasa a yaki da cin hanci da rashawa.

Ministan shari'a na Najeriyar, Barrister Abubakar Malami ya shaida wa BBC cewa duk wanda aka samu da laifin wawure kudin gwamnati za'a gurfanar da shi gaban kuliya.

Ya kara da cewa babu wata doka da gwamnatin kasar ke karyawa wajen tsarewa da kuma gurfanar da wadanda aka samu da laifin almundahana da cin hanci da rashawa.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta`annati a Najeriyar dai na binciken jami`ai da dama, kuma galibinsu na tsohuwar gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan, lamarin da ya sa wasu ke zargin cewa ana musu bi-ta-da-kulli ne irin na siyasa.