Nigeria: An dakatar da alkalan da ake zargi da cin hanci

Kungiyar lauyoyi ta Nigeria

Asalin hoton, EFCC

Bayanan hoto,

Kungiyar lauyoyi ta kasar ta nemi a dakatar da alkalan domin dawo da martabar shari'a a idon 'yan Nigeria

Hukumar da ke sa ido kan al'amuran shari'a a Najeriya NJC ta dakatar da wasu manyan alkalai bakwai daga aiki bayan da jami'an tsaro suka zarge su da karbar cin hanci da rashawa.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da direktan yada labarai na hukumar Soji Oye ya fitar a karshen wani taron da hukumar ta gudanar a Abuja.

Hukumar ta NJC ta ce an dakatar da alkalan ne har sai an kammala yi musu shari'a kan zargin aikata cin hanci da hukumar tsaro ta farin kaya, wato DSS ke musu.

A watan da ya gabat ne jami'an DSS suka yi dirar mikiya a gidajen alkalai a sassan kasar daban-daban, inda ta kama su.

Matakin na NJC ya zo ne bayan kiran da Kungiyar lauyoyi ta kasar ta yi na a dakatar da alkalan, tana mai cewa hakan ya zama wajibi matukar hukumar ta na so kimarta ta dawo a idanun 'yan kasar.