Ka san daliban jami'ar da suka fi kwazo a duniya?

Daliban Jami'ar Sydney

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Dalibai na murna a Jami'ar Sydney: Daliban jami'o'in Australiya sun fi na Burtaniya kokari

A kasashen duniya ana bayar da fifiko sosai a kan nagartar ilimin gaba da sakandare musamman na Jami'a.

A kasashen duniya ana fitar da rukunin jami'o'i da suka yi fice da suna wajen karantarwa da nagartar ilimin da suke bayarwa.

Wannan matsayi ya dogara ne a kan abubuwa da dama da jami'a ta shahara da su, kama daga tarihinta da yawan malamai idan aka kwatanta da yawan dalibai da kuma irin binciken da ake samarwa a jami'ar.

Sai dai kuma abin masu bayar da kima da fifita jami'o'in ba sa yi shi ne, duba kokarin da daliban da wadanan jami'o'i ke koyarwa suke da shi a fagen ilimi.

To amma a wani rahoto da take fitarwa na shekara-shekara, kungiyar hadin kai don cigaban tattalin arziki da bunkasa kasashe ta duniya, OECD, a bincikenta kan ilimi, ta fitar da matsayin kwazon daliban jami'o'i na kasashe daban-daban.

Kuma sakamakon ya saba da bambancin da ake gani na yadda wasu jami'o'i suke zaman na gaba a duniya, jami'o'in da yawancinsu suke a kasashen Amurka da Burtaniya, kamar su Harvard da MIT da Stanford da Oxford da Cambridge da UCL.

Abin mamaki binciken ya nuna cewa daliban da suka fi kwazo ba a jami'o'in Amurka ko Burtaniya suke ba, maimakon haka na Japan da Finland ne a gaba.

Wadannan alkaluman da aka tattara bisa jarrabawar da aka yi maimakon suna da shaharar jami'a sun nuna wadanda suke kan gaba ba 'yan kasashen da ake tsammani ba ne.

Daliban kasashe goma na farko da suka fi kwazo kamar yadda binciken na OECD, ya nuna su ne:

1,Japan 2, Finland 3, Holland 4, Sweden 5, Australia 6, Norway 7, Belgium 8, New Zealand 9, Ingila 10, Amurka

Ba daya daga cikin kasashen da suke kan gaba a wannan kwazo na dalibai, da ta yi fice sosai a jerin jami'o'in da suke sahun gaba a duniya wadanda suka yi suna.

Duk da cewa an san sunayen fitattun jami'o'in Amurka a duniya, amma kuma jami'o'in Norway da Australia kusan sun fi samar da dalibai da suka fi kkokari.

A jerin fitattun jami'o'in da ke kan gaba a duniya guda 100, 32 na Amurka ne, amma kuma daya ce kacal daga New Zealand. Kuma duk da haka daliban da suka kammala jami'a daga New Zealnad din sun fi takwarorinsu da suka yi jami'o'in Amurka ilimi.

Asalin hoton, IStock

Bayanan hoto,

Oxford ce ta daya a jami'o'in duniya a jadawalin Times Higher Education

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Akwai kuma maganar kudin da ake kashewa, misali ribar da ake samu daga kudin da aka zuba na bunkasa ilimin jami'a ko manyan makarantu.

Tsarin karatun jami'a a kasar Holland, duk da cewa ba shi da tsada sosai ko a ce ma yana da araha, amma kuma ilimin dalibansu ya fi na Amurka da Ingila wadanda ke karbar kudi masu yawa sosai daga dalibai.

Ba a sanya Scotland da Wales a wannan nazari na kungiyar ta OECD ba, amma Ireland ta Arewa tana mataki na 14 ne na jami'o'in da dalibansu suka fi kwazo a duniya.

Wannan bincike ya kara nuna yadda ba wai lalle kyakywan tsari na makaranta, dole ne a ce ya samar da ilimin da ya fi nagarta ba a jami'o'i.

Koriya ta Kudu da Singapore, dukkaninsu sun yi fice a jerin masu jami'o'in da suka fi suna a duniya, amma kuma su ma dalibansu na baya a sahun wadanda suka fi kokari a duniya.

To kuma me za a ce a kan darajar digirin jami'o'in a kasashe irin su Italiya da Spaniya da Girka, wadanda dalibansu suke can kasa-kasa a jerin wadanda suka fi kokarin?

Asalin hoton, iStock

Bayanan hoto,

Daliban jami'o'in Japan na daga wadanda suka fi kokari a duniya ( Jadawalin OECD)

Darektan harkokin ilimi na kungiyar ta OECD, Andreas Schleicher, ya ce sakamakon ya nuna yadda ake da bambancin hazaka ko kokari tsakanin mutanen da suke da takardar ilimi iri daya.

Zai iya kasancewa dukkaninsu suna da digiri, amma kuma a samu bambanci sosai na ingancin iliminsu.

Mista Schleicher ya ce, ''idan ana maganar karatun jami'a ne za ka fi samun ilimin digiri mai nagarta a Japan da Finland ko Holland, fiye da a jami'o'in Italiya ko Spaniya ko Girka.''

Asalin hoton, iStock

Bayanan hoto,

An samu sakamakon ne daga jarrabawar da aka yi wa dalibai, ba matsayin jami'a ba

Sakamakon wannan binciken na OECD, zai iya kasancewa sabanin tsarin fitar da jerin sunayen jami'o'in da suka fi nagarta a duniya.

Amma kuma ba za a iya cewa sakamakon binciken guda biyu, ba su da alaka ba, in ji Ben Sowter, daraktan hukumar da ke fitar da jerin sunayen jami'o'in da suka fi nagarta a duniya.

Yayin da binciken kungiyar ta OECD, ya yi gwajin nasa tsakanin tsarin jami'o'in kasashe, shi kuwa tsarin fitar da jami'o'in da suka fi inganci a duniya, yana mayar da hankalin bincikensa ne tsakanin wasu ffitattun jami'o'i kawai.

Mista Sowter ya ce, ''idan za a jarraba duk wata jami'a ta Amurka za a ga cewa tana da daliban da suke cikin rukunin wadanda sukafi kokari sosai da kuma wadanda suka fi rashin kokari.''

Amurka tana da tsarin ilimi da ya bambanta sosai da juna, amma wannan ba ya nuna bambancin karara kamar yadda tsarin fitar da jerin jami'o'in da suka fi wanda yake mayar da hankali kan jami'o'in da suke sama kawai.

Ga jerin sunayen jami'o'in da ke kan gaba a duniya na shekarar 2016-17 (QS World University Rankings);

1,Massachusetts Institute of Technology (MIT)

2,Stanford University

3,Harvard University

4,Cambridge University

5,California Institute of Technology (Caltech)

6,Oxford University

7,University College London

8,ETH Zurich

9,Imperial College London

10,University of Chicago

Mista Sowter ya ce nasarar kasa kamar Finland a irin daliban da take samarwa masu nagarta, hakan ya jibanci tsarin makarantarta ne, da kuma na jami'o'inta.

Domin zai fi wuya ka iya gudanar da jami'a maras kyau a Finlnad, idan ka kwatanta da Amurka.

Ma'ana abu ne mai sauki ka iya gudanar da jami'a maras inganci a Amurka, amma da wuya ka iya yin hakan a Finland.

Amma kuma Mista Sowyer ya ce, binciken na OECD, ya kara fito da tambayar da aka dade ana yi kan abin da ya kamata a ba fifiko a ilimin jami'a.

Cewa, shin gwamnatoci za su zuba kudi ne da bayar da mmuhimmanci don ganin an samu ilimi mai nagarta gaba daya a jami'o'in ko kuma za su mayar da hankali ne wajen samar da jami'o'i 'yan kalilan da suka fi inaganci?

Tsarin fitar da sunayen jami'o'in da suka fi kyau zai iya nuna bambanci tsakanin daidaikun jami'o'i, amma kuma Mista Sowter, ya ce ba za a iya amfani da wannan tsari ba wajen auna yadda tsarin ilimin jami'a ke gudana, da kyau ko ba kyau.

OECD ta gudanar da bincikenta ta hanyar jarrabawa tsakanin makarantun sakandare na sama da kasashe 70.

Daga nan ne kuma kwararrun suka yi kokarin amfani da irin wannan tsari na binciken a kan jami'o'i ta yadda za a iya bambancewa tsakanin jami'o'i daidaiku.

Asalin hoton, iStock

Bayanan hoto,

Jami'o'i irin su Harvard su ne kan gaba a jerin sunayen na daya a duniya

Sai dai kuma jami'o'i a Amurka, ko alama ba su nuna sha'awa a kan hakan ba, saboda haka babu wani sakamako na jerin jami'o'in da suka fi inganci ta hanyar kwazon daliban da suke samarwa.

Duk da cewa akwai tababa a game da ainahin tartibin tsarin da za a bi wajen fayyace jami'o'in da ke kan gaba, ba za a iya cewa hakan ba shi da muhimmanci ba, tun da dai jami'o'i har suna gogayya tsakaninsu.

Lokacin da Jami'ar Oxford ta zama ta daya a karon farko a wannan shekara a jerin sunyen jami'o'in da suka fi a duniya (na Times Higher Education), abin sai ya zama babban labari.

To amma kamar yadda wannan bincike na OECD shi kuma ya nuna, kamata ya yi a ce daliban jami'o'in kasashen Japan da Finland suna daga cikin masu wannan murna.