Wani Matashi a Kano ya hada mota mai amfani da hasken rana

  • Mukhtar Adamu Bawa
  • BBC Hausa
Mota mai amfani da hasken rana
Bayanan hoto,

Fasahar mota ce yadda ba za ta dinga fitar da hayaki ba

Wani matashi a birnin Kano na arewacin Najeriya ya kirkiri wata mota mai amfani da makamashin hasken rana a maimakon man fetur.

Matashin, Mukhtar Adamu Fasaha, dan shekara 23 ya ce motar, wadda ta yi tafiyar sama da kilomita 1 a wani gwaji da ya yi, an hada ta ne da karafa da katakai da batur da faifan zuko hasken rana.

Ya ce faifan, wanda ya yi wa motar rumfa, shi ne yake bai wa batirin motar wuta.

Tana kuma amfani da wani moto irin na injin jawo ruwa wanda yake samun wuta daga batirinta, sannan ya juya kundun giya, ta yadda tayoyinta za su fara tafiya.

An sanya wa motar kundun giya da tayoyin babur Vespa, kuma ana iya inganta fasahar wajen rage dogaro da man fetur zuwa amfani da makamashi maras gurbata muhalli, don harkokin sufuri a kasashen Afirka kamar Nijeriya.

A cewar matashin, idan akwai kayan aiki, ana iya inganta ta, a fadada ta, a musanya katakan da ke jikinta da karfe yadda za ta fi karko da jan hankali.

Mukhtar ya kuma ce ya shafe kimanin shekara biyu yana tara kayan hada motar, amma a cikin kwana 11 ya hada ta.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

"Akwai abubuwan da za a iya saukaka ta'ammali da man fetur din kamar irin wadannan (motoci) in aka yi su manya-manya haka. Ka ga an samu sauki ma ke nan", inji shi.Mota mai amfani da hasken rana a Kano

Motar mai fadin inci 40 da tsawon inci 72 tana da mazaunin mutum biyu ne amma matashin ya ce tana da karfin daukar mutum hudu. Ya ce ya sayi kayayyaki da dama, wasu kuma ya tsince su don hada wannan mota da ke iya tafiya har ma da baya da baya.

An sauya fasalin moto dinta daga ainihin karfin voltage 480 da yake da shi zuwa voltage 360 ko 240 ta yadda batirin da aka sa mata zai iya dadewa yana aiki ba tare da ya ja lantarki mai yawa ba.

Matashin ya ce idan aka sa wa motar ingantaccen batir mai karfi zai iya ba ta wutar da za ta yi gudu a lokaci guda kuma ta adana wani bangare na lantarki ko da za a shiga yanayin da ba hasken rana.

Ya kuma ce an tsara fasahar motar ce yadda ba za ta dinga fitar da hayaki ko yin wata k'ara ba, amma saboda ba a goge kacar da aka sanya mata ba, tana yin guga.

Ya zuwa yanzu ba a tantance gudun kilomita nawa take iya yi a cikin sa'a guda ba, amma dai makerin motar ya ce zai yi hakan a nan gaba idan ya sauya mata batir.

Da haka kasashe suke cigaba

Bayanan hoto,

Mukhtar ya ce motar, wadda ta yi geajin tafiyar kilomita daya, za ta iya daukar mutum hudu

Najeriya na da dumbin hazikan matasa irinsu Mukhtar Fasaha masu kirkirar abubuwa iri daban-daban, sai dai ba su cika samun tallafi don bunkasa irin wadannan fasahohi na cikin gida ba.

Makerin motar ya ce da tallafa wa mutane masu fasahar kirkire-kirkire kasashe suke ci gaba.

A cewarsa, idan aka tallafa to kasa za ta rika kirkirar abubuwa nata na kanta, ba sai ta dogara an shigar mata da wasu abubuwa daga waje ba.

"Rashin kudi ya hana ni cigaba da karatu"

Mukhtar Fasaha, wanda ya ce rashin samun tallafi ya hana shi ci gaba da karatu, ya halarci makarantar firamare ta Maimuna Gwarzo a Kaduna. Daga nan ya wuce zuwa karamar makarantar sakandaren Digital Science, kafin ya koma Kano wajen mahaifinsa a shekara ta 2010.

Ya ce yana gyaran rediyo da wayar salula, kuma ya taba kera taransimitar rediyo har ma ya dinga yada shirye-shirye kuma ya hada inverter ta gida.

Matashin ya ce a yanzu haka shi yaron shago ne a kasuwar Kantin Kwari.