Hong Kong: China ta hana wdansu 'yan majalisa kama aiki

'Yan majalisar dokokin Hong Kong

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Yau Wai-ching (hagu) da Sixtus Leung (dama) sun ki yin mubaya'a ga Beijing

Kasar China ta dauki matakai na ba-zata a kan harkokin siyasar yankin Hong Kong na hana wadansu 'yan majalisa biyu kama aiki.

'Yan majalisar masu goyon bayan samun 'yancin cin-gashin kai, Sixtus Leung da Yau Wai-ching, sun ki amincewa su yi mubaya'a ga kasar China a yayin rantsar da su.

Chinar na yi wa wani bangare na dokar Hong Kong iyakar cewa, duk wani jami'i da bai sha cikakkiyar rantsuwar kama aiki ba za a haramta masa shiga ofis, kamar yadda wata kafar yada labarai a kasar ta bayyyana.

Matakin na zuwa ne bayan rudanin da aka shafe makonni ana yi a majalisar dokokin kasar ta Hong Kong.

'Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla wajen tarwatsa masu zanga-zangar a wajen ofishin hulda da jama'a na yankin Hong Kong, tare da cafke akalla mutane hudu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan sanda a Hong Kong sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla kan masu zanga-zanga ranar Lahadi

Yankin Hong Kong yanki ne mai cin gashin kai a wasu bangarorin a karkashin kasa guda, amma kuma a bisa tsare-tsaren mulki biyu tun bayan da ya koma China a shekara ta 1997.

Amma kuma a kundin tsarin mulkin yankin, da muhimman dokoki sun tanadi cewa kasar China ce za ta rika bayar da shawara ta karshe a kan yadda za a yi amfani da dokokin.

Yankin na Hong Kong na kallon katsalandan din kasar China a matsayin wani babban kalubale ga 'yancin fadin albarkacin baki da na harkokin shari'a.

Ana kuma kallon duk wani batu kan 'yancin cin-gashin kai a matsayin wata barazana.