WHO: Mutane fiye da 7,000 suka mutu a yakin basasa a Yemen

Yemen yaki

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Yakin basasa a kasar Yemen ya haddasa lalacewar gine-ginen asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya

Wani bincike da kungiyar lafiya ra duniya WHO ta gudanar ya gano cewa yakin basasa a kasar Yemen ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da dubu bakwai.

An kuma jikkata wasu mutane 37,000 a rikicin, wanda aka soma a bara.

WHO tace fiye da rabin cibiyoyin lafiyar Yemen din basa aiki yadda ya kamata ko kuma suna rufe.

Kana likitoci sun ce mutane da dama na mutuwa sakamakon ja'ibar yunwa.

Yakin ya jefa kasar cikin mawuyacin hali na tabarbarewar tattalin arziki.

Yemen na daya daga cikin kasashe masu fama da talauci a duniya.