Mun fasa karbar bindigogi daga Amurka- Duterte

Mr Duterte ya ce sun fasa siyo bindigogi daga Amurka
Shugaban kasar Philippines,Rodrigo Duterte ya ce ya bayar da umarnin a soke kwangilar siyan dubban bindigogi daga Amurka.
Mr Duterte ya ce kasar sa zata duba zabi mafi sauki.
Fiye da bindigogin Amurka dubu ashirin da biyar ne ake sa ran za a bawa 'yan sandan Philippines.
Dangantaka tsakanin kasashen biyu dai wato Amurka da Philippines ta yi tsami tun bayan hawan Mr Duterte kan mulki.
Akwai dai rahotannin da ke cewa Amurkan ma na shirin fasa kai bindigogin kasar ta Philippines saboda damuwar da ta ke da ita kan tsauraran matakan da Mr Duterte ya dauka a kan masu safarar miyagun kwayoyi.
Babban Labari
Minti Daya Da BBC
Saurari, MINTI ƊAYA DA BBC NA YAMMA 20/01/2021, Tsawon lokaci 1,00
MINTI ƊAYA DA BBC NA YAMMA 20/01/2021