Dakarun Kurdawa sun kutsa garin Bashiqa dake hannun IS

Iraqi Bashiqa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Dakarun Peshmarga na lugudan wuta kan yankin mayakan IS yayin da suke kara dannawa cikin garin Bashiqa

Dakarun Kurdawan Iraqi sun kutsa kai cikin garin Bashiqa wanda mayakan IS ke rike da iko dake arewa maso gabashin birnin Mosul.

Hayaki ya rika tashi sama lokacin da ake arangama tsakanin dakarun Peshmerga da na kungiyar IS a garin na Bashiqa.

Da safiyar Litinin ne daruruwan mayakan Peshmerga da ke samun goyon hare-haren dakarun kawancen da Amurka ke jagoranta ta sama, sun kara dannawa cikin garin daga kusurwowi uku.

Rundunar sojin Iraqi ta ce ta gano wani wagegen kabari da aka cika da gawarwakin mutane 100 a kudancin birnin Mosul.

An haka kabarin ne a harabar makarantar koyon ayyukan gona dake wajen garin Hamam al-Alil, da dakarun suka shiga a cikin karshen mako.

A shekarar 2014, mayakan sun kai hari kan kananan kabilu da jami'an tsaro a yankin, lokacin da suka kutsa ta cikin arewacin Iraqi bayan da suka karbe iko da birnin Mosul.

Majalisar Dinkin Duniya ta samu rahoton cewa masu tada kayar bayan sun yi ta tafka ta'asa tun lokacin da gwamnatin Iraqi ta fara yunkurin sake kwato birnin na Mosul makonni uku da suka gabata.

An yi zargin cewa a ranar 29 ga watan Oktoba sun hallaka tsoffin sojoji na yakunan Hamam al-Alili da Shura su 40, kana suka jefa gawarwakinsu cikin kogin Tigris.

Akwai kuma bayanan da suka nuna cewa mayakan na IS sun haka hanyoyin karkashin kasa da dama a fadin garin na Bashiqa.