Masu tada kayar baya sun fasa bututun mai a Niger Delta

Yankin niger Delta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yankin Niger Delta ya kwashe shekaru da dama yana fama malalar mai dake gurbata musu muhallansu.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce masu tada kayar baya sun fasa wani bututun mai mallakar jihar Delta a garin Warri.

Wasu masu gadi a Bututan man na kamfanin Trans Forcados, sun sha da kyar bayan da mayakan sa kan suka bude musu wuta, kamar yadda Dickson Ogugu shugaban al'ummar Batan ya shaida wa AFP.

Rahotanni daga kamfanin dilancin labaran ya ce wani jami'in soja ya tabbatar da harin.

A makon da ya gabata an fasa bututun bayan shugaba Muhammad Buhari ya gana da wakilan kungiyar masu tada kayar baya na yankin Niger Delta a wani yunkuri na kawo karshen rikicin yankin.

Kungiyar dai ta bukaci gwamnati ta kashe akasarin kudin da Najeriya ta ke samu daga mai wajen magance matsalar talauci, kuma ta dauki matakai wajen kawo karshen malalar mai da ke lalata muhallan yankin.