Dalilai biyar da suka sa Trump ya yi nasara

Dan takarar jam'iyyar Republican Donald Trumpya halarci wajen yakin neman zabe a Wilmington, Ohio.

Asalin hoton, Reuters

Donald Trump ya bayar da mamaki sosai tun daga farkon lokacin da ya shiga takarar neman shugabancin Amurka shekara daya da ta wuce.

Mutane kalilan ne suka yi tsammanin zai iya yin takarar, amma kuma sai ga shi ya yi. Ba su yi zaton zai yi nasara a zaben ba, sai kuma ya yi. Sun ce ba zai ci zaben fitar da gwani na jam'iyyar Republican ba, amma ya lashe zaben.

Da karshe sai suka ce babu yadda zai iya fafatawa a zaben ballantana ma ya yi nasara a babban zaben.

Yanzu dai Donald Trump shi ne zababben shugaban kasar Amurka.

Ga abubuwa biyar da suka sanya ya yi ba-zata, har ya lashe zaben na shugaban kasa:

Farar-fatar Amurka sun fi son Trump

Dan takarar jam'iyyar Republican Donald Trump ya hada gagarumin yakin neman zabe a dandalin J.S. Dorton ranar bakwai ga watan Nuwamba, 2016 in Raleigh, a North Carolina

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Donald Trump ya nuna adawa da baki a lokacin yakin neman zabe

Kamar a mafarki, manyan jihohi daya bayan daya irin su Ohio, Florida da kuma North Carolina sun zabi Mista Trump.

Hakan ya sa Misis Clinton ta yi faduwar bakar-tasa.

Fatan 'yan jam'iyyar Democrat na karshe shi ne su yi nasara a jihohin tsakiyar yammacin kasar. Su ne jihohin da jam'iyyar ta kwashe shekara da shekaru tana cin zabe, saboda yawancin mazaunansu bakar-fata ne da kuma farar-fata ma'aikata.

Yawancin farar-fatar, musamman wadanda ba su da ilimi - maza da mata - sun kauracewa jam'iyyar.

Su kuwa masu kada kuri'a da ke karkara sun fito kwansu-da-kwarkwata musamman ganin yadda suke jin haushin cewa attajirai sun yi watsi da su.

Kodayake jihohi irin su Virginia da Colorado sun zabi Cliton, amma ta sha kaye a Wisconsin - kuma hakan ya yi sanadin faduwarta.

Idan aka yi la'akari da yadda al'amura suka gudana, za a iya cewa Misis Clinton za ta iya cinye zaben California da New York saboda yawan goyon bayan da take da shi a can, sai dai ta sha mamaki a jihohi irin su Utah.

Guguwar Trump ta mamaye wadannan jihohin.

Yadda Donald Trump ya samu nasarar zama shugaban kasa

Manhajar intanet dinka ba ta daukar irin wadannan bayanan. Dole ne ka mallaki manhaja ta zamani wacce ke amfani da Javascript domin ganin wannan shafin.

Donald ba ya ganin kowa ga gashi

Masu son yi wa Republican takara (L-R) Gwamnan Wisconsin Scott Walker, Donald Trump da kuma Jeb Bush sun yi muhawararsu ta farkowacce gidan talabijin na FOX News and Facebook suka hada a dandalin Quicken Loans a Cleveland, Ohio.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Trump ya sha sukar yadda ake tafiyar da al'amura a Amurka

Mr Trump ya zagi fitaccen tsohon sojan nan da ya yi wa Amurka yaki John McCain.

Ya yi fada da gidan talabijin na Fox News da fitacciyar mai gabatar da shirin nan Megyn Kelly.

Ya nemi fada a lokacin da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya zolayi sarauniyar kyau 'yar Hispania saboda tebarta.

Bai yi da-na-sani ba lokacin da aka fitar da wani bidiyo da ke nuna shi yana neman yin lalata da wasu mata.

Sau uku yana yin mummunar katobara a lokacin muharawar da suka yi da abokiyar takararsa.

Amma duk da wadannan batutuwa, sai ga shi an zabe shi.

Farin-shiga

Magoya baya sun rike alamomi da kuma littafin Linjila a wajen yakin neman zaben dan takarar Republican Donald Trump, ranar 7 ga watan Nuwamba na 2016, a Manchester, N.H.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Mafiya yawan mabiya addinin Kirista Donald Trump suka zaba

Ya fafata da 'yan Democrat. Kazalika ya kalubalancin masu ruwa da tsaki a jam'iyyarsa.

Kuma ya yi nasara a kansu.

Mr Trump ya yi wasu dabaru da suka karya lagon abokan takararsa na zaben fitar da gwani na Republican. Wasu daga cikin su, kamar Marco Rubio, Ted Cruz, Chris Christie da Ben Carson, sun bayar da kai bori ya hau.

Wadanda kuma ba su mika wuya ba, irin su Jeb Bush da gwamna Ohio John Kasich, sun zama 'yan kallo.

Haka kuma sauran manyan 'yan jam'iyyar da ba su goyi bayansa ba, kamar kakakin majalisar wakilai Paul Ryan ba su da wani tasiri domin Mista Trump ba ya bukatar taimakonsu a yanzu.

Hasalima, ana ganin ya ci zabe ne saboda ya ce zai karya kashin bayansu.

Rawar da FBI ta taka

Shugaban FBI James Comey ya taka rawa wajen cin zaben Trump

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wasu sun soki shugaban FBI James Comey da cewa ya taka rawa wajen cin zaben Trump

Da alama kuri'ar jin ra'ayoyin jama'ar da aka yi ba ta yi amfani ba, musamman idan aka yi la'akari da sakamakon zaben jihohin tsakiyar yammacin kasar.

Ta fito fili cewa a lokacin da aka kusa yin zaben, kuri'un sun nuna cewa 'yan takarar biyu suna kankankan, kuma daga karshe an ga yadda Mr Trump ya yi nasara.

Sai dai alamar yin nasararsa ta bayyana sosai ne makonni biyu kafin zaben, kafin ma shugaban hukumar bincike ta FBI James Comey ya sake bude batun binciken sakonnin email din Hillary Clinton.

A zahiri, kuri'ar jin ra'ayin jama ta nuna cewa suna kankankan, amma farin-jinin Mr Trump ya karu sosai ne tsakanin lokacin farko da FBI ta ce za ta binciki Clinton da kuma lokaci na biyu da ta sake tayar da maganar.

A lokacin ne Mista Trump ya karfafa irin goyon bayan da yake da shi, kodayake shi kan sa Comey bai tsira daga suka daga wajen Trump ba.

Trump ya yarda da kansa

Dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican Donald Trump ya hau kan mumbari a wajen yakin neman zabe na ranar 5 ga watan Nuwamba na 2016, a Reno da ke Nevada

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Donald Trump ya gagari kowa a fagen siyasar Amurka

Mr Trump ya fafata ne a yakin neman zaben da ba kasafai ake yin irinsa ba, kuma hakan ya ba shi dama ta musamman.

Ya mayar da hankalinsa ne kan yadda zai ja magoya bayansa a jiki, maimakon yin la'akari da kuri'ar jin ra'ayin jama'a.

Ya ziyarci jihohi irin su Wisconsin da Michigan wadanda masu fashin-baki suka ce ba zai iya lashe wa ba.

Ya gudanar da manya-manyan tarukan yakin neman zabe a madadin bi gida-gida yana neman kuri'a.

Kudaden da Clinton ta kashe wajen yakin neman zabe sun ninka nasa ba sau daya ba, kamar yadda mutanen da suka yi takarar fitar da gwani da shi a jam'iyyar Republican suka fi shi kashe kudade.

Sai dai yana da wani siddabaru na jan hankalin mutane ta hanyar kalamansa na kin jinin mutanen.

A karshe dai, bukatarsa ta biya - kuma shi da iyalinsa da kadan daga masu ba shi shawara - su ne za su shiga fadar White House.