An yi asarar $600bn saboda boren da aka yi a kasashen Larabawa

Wani mai zanga-zanga yana jefa kwanson hayaki mai sanya hawaye a birnin Alkahira na Masar

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

An soma boren ne a shekarar 2011.

Juyin-juya-halin da aka yi a kasashen Larabawa ya sanya yankin ya yi asarar kusan $614, in ji wata hukuma ta majalisar dinkin duniya.

Wannan kiyasi shi ne na farko da aka yi kan tasirin da boren ya yi a fannin tattalin arzikin yankin.

Hukumar da ke nazari kan tattalin arziki da walwala a yankin yammacin Asia ta ce asarar ta yi daidai da kashi shida na kudaden da kasashen Larabawa za su samu daga shekarar 2011 zuwa 2015.

Boren, wanda aka soma daga kasar Tunisia, ya ci rawanin shugabanni kasashe hudu, kuma ya haddasa rikici a kasashen Libya, Syria da kuma Yemen.

Hukumar ta yi kididdiga kan irin kudaden da take ganin yankin zai samu da a ce ba a yi juyin-juya-halin ba kafin ta fitar da wadannan bayanai.

Ta sanya kasashen da rikicin bai shafa kai-tsaye ba a cikin rahotonta, saboda irin tasirin da faruwar rikicin ya yi a kan su.