Nigeria: Buhari ya rantsar da sabon alkalin alkalai

Asalin hoton, Nigerian Government
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da Walter Onnoghen a matsayin alkalin alkalan kasar na riko.
Mista Onnoghen ya maye gurbin mai shari'a Mahmud Mohammed wanda ya yi ritaya a ranar Laraba.
An yi bikin rantsuwar ne a fadar shugaban kasar da ke Abuja.
Mai shari'a Walter Onnoghen ya karbi wannan mukami ne a daidai lokacin da fannin shari'ar kasar ke cikin mawuyacin hali saboda zargin cin hanci da rashawa.
A watan da ya gabata ne jami'an tsaro suka kame wasu manyan alkalai bakwai a wani bangare na binciken da ake yi.
Hukumomi sun ce sun gano dubban daloli a gidajen alkalan, wadanda aka bayar da belinsu, amma har yanzu ba a tuhume su a kotu ba.
Batun dai ya raba kan lauyoyi da sauran masu ruwa da tsaki a fagen shari'ar kasar.