Ivory Coast ta hana sayar da giya a leda

Barasar Leda

Asalin hoton, RTI Officiel

Bayanan hoto,

Ivory Coast ta ce ta dauki matakin ne domin inganta lafiyar 'yan kasar

Kasar Ivory Coast ta hana sayar da barasar da ake durawa a cikin leda kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin kasar, Bruno Kone ya ce.

Sananniyar giyar ledar na zuwa ne a samfuri daban-daban kamar giyar rum, vodka ko kuma wasu da ake sayarwa daga farashin sefa 200 zuwa sefa 1,000.

Mista Kone ya ce gwamanti ta hana sayar da barasar ledar ne bisa dalilian lafiya, da kuma hana mutane kasancewa 'yan maye.

Mutane sun mayar da martani da dama a kan sanarwar, wacce kamfanin yada labarai na kasa ya fitar a shafinsa na Twitter.

'Yan kasar suna shakkun ko da gaske gwamnati za ta aiwatar da hukuncin.