Soyinka ya ce zai bar Amurka ranar da Trump ya karbi mulki

Wole Soyinka

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Green Card dai kati ne na dindindin da ke bai wa mutum damar zama a Amurka

Shahararren marubucin nan na Nigeria Wole Soyinka ya ce zai bar Amurka a ranar da aka rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban kasa.

A wani martani da ya mayar na sakonnin imel da aka aike masa, Soyinka ya ce a ranar 20 ga watan Janairu na shekarar 2017, "ku kalli ficewa ta daga Amurka".

Mujallar Newsweek da ke Amurka ta ce zai kasance a kasar har sai Trump ya sha rantsuwa.

Ta kara da cewa, "An ambato Soyinka yana cewa "me ya sa ba za a jira har sai Trump ya karbi ragamar mulki ba?

"Ina aikace-aikacena na yau da kullum, amma kuma ba zan kara yin wasu ayyukan ba. A halin yanzu dai mu tsaya a kan hakan."

A makon da ya gabata ne dai Mista Soyinka ya yi alkawarin cewa zai yaga takardar izinin zamansa a Amurka, wato Green card idan Mista Trump ya yi nasarar zabe.

Kalamansa dai sun bayyana ne a wata tattaunawar bidiyo da ya yi da dalibai wadda aka nada a Jami'ar Oxford da ke Biritaniya.

Wole Soyinka dai ya yi hakan ne a matsayin wani martani ga tsauraran matakan da Donald Trump yake so ya dauka kan shiga da fita Amurka.