Obama ya gana da Donald Trump a White House

Shugaba Barrack Obama tare da Donald Trump

Asalin hoton, EUROPEAN PRESS AGENCY

Bayanan hoto,

Shugaba Barrack Obama tare da Donald Trump a fadar White House

Shugaban Amurka Barrack Obama ya tattauna da sabon shugaban kasar da aka zaba na jamiyyar Republican Donald Trump a fadar White House.

Shugaba Obama ya ce sun tabo batutuwa da dama a tattaunawar da suka yi wadanda suka hada da batun cikin gida da kuma manufofin kasar kan kasashen waje.

Ya kara da cewa yana son Mr Trump da matarsa su ji cewa sun sami kyakkyawar maraba inda ya jaddadawa zababben shugaban kasar cewa za su yi duk abinda za su iya yi domin taimaka masa yin nasara.

Shi ma a nasa bangaren Mista Trump ya ce sun tattauna kan batutuwa da dama wasu daga ciki masu kyau ne yayin da wasu kuma masu sarkakiya sosai.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Wannan ne karon farko da Obama ke ganawa da Donald Trump bayan zaben shugaban kasar

Tun da farko da yake jawabi ranar Laraba bayan da aka sanar da sakamakon zaben, Mista Donald Trump, ya ce zai saka muradun Amurka gaba da komai, amma zai yi adalci ga kasashen da ke da sha'awar tafiya tare da Amurka.

Mista Trump ya lashe zaben ne bayan da ya samu kujerun wakilai sama da 270 a jihohi 50, a inda ya kayar da abokiyar hamayyarsa Hillary Clinton.

Trump, wanda ya gabatar da jawabin amincewa da yin nasara, ya ce Clinton ta kira shi ta wayar tarho inda ta taya shi murnar lashe zaben.

A cewarsa, zai mayar da hankali wajen ganin ya sake gina Amurka, yana mai cewa muradin kasar su zai sanya farko a kan komai.