'Jacob Zuma ya tsallake rijiya da baya'

Karo na uku kenan da jamiyyar ANC mai mulki ke dakile yunkurin kada kuri'ar yanke kauna akan shugaba Zuma

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Karo na uku kenan da jamiyyar ANC mai mulki ke dakile yunkurin kada kuri'ar yanke kauna akan shugaba Zuma

Shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma ya tsallake kuri'ar yanke kauna da 'yan Majalisar dokoki suka kada a kansa.

Babbar jami'yyar adawa ta Democratic Alliance ita ce ta gabatar da kudurin kan abin da ta kira sakacin da yake yi a shugabancin kasar.

Jamiyya mai mulki ta ANC da ke da rinjaye a Majalisar ta goyi bayan shugaba Zuma.

Wakiliyar BBC ta ce wannan shi ne karo na uku a wannan shekarar da aka kada kuri'ar yanke kauna akan shugaba Zuma kuma jamiyyar ANC mai mulki dake da rinjaye a majalisar dokoki ta shawo kansu ba tare da wata matsala ba.