Rooney na so Southgate ya zama kocin Ingila na dindindin

Southgate da Rooney suna dasawa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Southgate ya taka rawar gani

Kyaftin din Ingila Wayne Rooney ya ce ya kamata a tabbatar wa kocin riko na kasar Gareth Southgate da mukaminsa.

Southgate ya ci wasa biyu cikin uku bayan tawagar kasar ta doke Scotland a wasan neman cancanrtar shiga gasar cin kofin duniya da suka yi a Wembley.

Rooney ya ce Southgate "Ya yi bakin kokarinsa kuma ina ganin shi ne a kan gaba" wajen zama koci na dindindin.

Yanzu dai Ingila ce a kan gaba a rukunin F bayan wasa hudu da ta yi kuma shi kan sa Southgate ya ce ya yi dadin kasancewarsa kocin kasar.

An bai wa Southgate mukamin ne bayan Sam Allardyce ya sauka daga kan mukamin.

Ya ce ya cika alkawarin da ya yi wa hukumar kwallon kafar kasar cewa zai tabbatar Ingila ce a kan gaba a rukunin F.