Brazil ta lallasa Argentina da ci 3-0

Neymar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Kwallon da Neymar ya zura a raga ita ce ta 50 da ya ci wa kasar

Neymar da Philippe Coutinho kowannen su ya zura kwallo guda a wasan da Brazil ta doke Argentina da ci 3-0 a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta 2018.

'Yan wasan Argentina, cikin su har da Lionel Messi sun yi kokarin yin tasiri a wasan, sai dai Paulinho ya zura tasa kwallon.

Yanzu dai Argentina tana mataki na shida a cikin tawaga 10 daga yammacin Amurka da ke son shiga gasar cin kofin duniya, kuma tuni hudu daga cikin su suka cancanci shiga gasar.

Argentina tana da makin 16 a wasa 11 da ta buga, wato tana bayan Ecuador, wacce take ta hudu da maki daya, kuma ita ce ta takwas a bayan Brazil, wacce ke da maki 24