Nigeria: kwastam ta koka kan kashe jami`anta

Shugaban hukumar kwastan Kanar Hamid Ali mai ritaya
Bayanan hoto,

Shugaban hukumar kwastan Kanar Hamid Ali mai ritaya

A Najeriya, hukumar hana fasa kwauri ta kasar wato kwastan ta koka da yadda take asarar jami`anta a yakin da suke yi da masu fasa-kwauri.

Hukumar ta ce a wannan shekarar kadai jami`anta sama da 70 ne suka rasu a irin wannan arangamar.

A wata hira da BBC shugaban hukumar Kanar Hamid Ali mai ritaya ya yi zargin cewa wasu jama'a a tsakanin al`umomin da ke kan iyakokin kasar na taimaka wa masu fasa-kwaurin.

Hukumar ta ce mutane da dama basu dauka fasa kwauri babban laifi bane.