Uganda: An yanke wa jami'an gwamnati hukuncin dauri saboda fansho

Shugaba Yuweri Musebeni

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kotu ta samu jami'an gwamnatin da cinye kudaden fansho

An gurfanar da manyan jami'an gwamnatin Uganda uku gaban kuliya, da ake zargi da laifin yin al'mubazzaranci da kudaden fansho kusan dala miliyan ashirin da biyar.

Wata kotu a birnin Kampala ta samu bayanin da ke cewa jami'an sun bude sama da asusu a banki dubu biyu da sunayen bogi, daga bisani kuma suke rarraba kudaden a lalitarsu.

An dai yanke musu shekara 10 kowanne a gidan kaso, amma suna da damar daukaka kara.

A bangare guda kuma za a yankewa wasu kananan ma'aikata biyar hukunci irin wannan duk dai kai batun.