Ban sanya ranar da zan yaga katin zama a Amurka ba - Soyinka

Wole Soyinka

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Green Card dai kati ne na dindindin da ke bai wa mutum damar zama a Amurka

Shahararren marubucin nan na Nigeria Wole Soyinka ya ce bai sanya ranar da yaga takardar izinin zamansa a Amurka, wato Green card ba.

A wata sanarwa da ya fitar, Mista Soyinka ya yi kakkausan suka ga masu mu'amala da shafukan intanet da na sada zumunta, wadanda ya ce su suka yi masa ƙage cewa ya ce zai bar Amurka a ranar da aka rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban kasa.

Sanarwar ta kara da cewa, "Bari na yi kashedi ga masu amfani da intanet: su sani cewa wataƙila ba a ƙyamar kasarsu Trump kamar yadda ake ƙyamar Najeriya wacce aka tilasta mana zama a cikin ta.

"Ya kamata su koma makaranta ku nemi ilimi. Halilci shi ne babbar matsalarku, domin shi yake sanya wa kuna tsoma baki a sha'anin da bai shafe ku ba."

Soyinka ya jaddada cewa zai yaga takardarsa ta izinin zama a Amurka, yama mai cewa zai yi hakan ne a lokacin da ya ga dama.

Shahararren marubucin dai ya gamu da sukar masu amfani da shafukan sada zumunta ne tun da aka ga bai bar yaga katin ba kamar yadda ya yi alkawarin yi idan Donald Trump ya lashe zaben shugaban Amurka.

Mako biyu da suka wuce ne dai Mista Soyinka ya yi alkawarin cewa zai yaga takardar izinin zamansa a Amurka, wato Green card idan Mista Trump ya yi nasarar zabe.

Ya yi alkawarin ne a tattaunawar bidiyo da ya yi da dalibai wadda aka nada a Jami'ar Oxford da ke Biritaniya.

Wole Soyinka dai ya yi hakan ne a matsayin wani martani ga tsauraran matakan da Donald Trump yake so ya dauka kan shiga da fita Amurka.