Shugaban FBI ne ya yi min kafar-ungulu —Clinton

Hillary Clinton

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Hillary Clinton ta kira Donald Trump ta taya shi murnar lashe zabe

Hillary Clinton ta zargi shugaban hukumar FBI James Comey, da taka muhimmiyar rawa a shan kayen da ta yi a zaben shugaban kasa da aka kammala a makon da ya wuce.

Misis Clinton ta shaida wa jiga-jigan jam'iyyarta ta wayar tarho cewa sanarwar da Mista Comey ya yi cewa ba ta da laifi a kan batun amfani da emel dinta a lokacin da ta ke Sakatariyar harkokin wajen Amurka a kurarren lokaci shi ya karyar kwarin gwiwar magoya bayanta.

Ta yi wannan bayani a daidai lokacin da dubban Amurkawa a sassa daban daban ne ke ci gaba da yin boren kin amincewa da Mista Trump a matsayin shugaban kasa.

A birnin New York 'yan sanda sun yi kokarin hana masu zanga-zangar isa dandalin Union da wasu kuma na daban da suka tunkari gidan Mista Trump da kuma dogon ginin Trump Towers da hedikwatar kasuwanci da ke birnin.

Kuma da alama shi kansa Trump ya sassauta matsayinsa kan wasu batutuwa da ya sha alwashin aiwatarwa idan ya lashe zaben.

MistaTrump ya ce zai ci gaba da aiwatar da shirin Shugaba Obama na inshorar lafiya duk da cewa a baya ya bayyana shirin a matsayin wani babban bala'i ga kasar.